Sojoji sun kama makamai a Bauchi

soja Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu sojojin Najeriya akan titi

Hukumomin tsaro a jihar Bauchin Nijeriya sun yi Karin bayani kan wata mota da suka kama a jiya dauke da muggan makamai da suka hada da bama-bamai, da bindigogi da albarusai a dab da garin Alkaleri.

Motar dai ta fito ne daga ta Gombe kan hanyarta ta zuwa garin Bauchi.

Hukumomin tsaron dai sun bayyana cewa wadanda ke tafe a motar sun gudu suka shiga daji a yayin da aka tare motoci a wani wurin binciken ababan hawa kuma kawo yanzu ba a kama su ba.

A Nijeriya dai an sha kama mutane dauke da muggan makamai, amma ba kasafai ake ganin ana hukunta su a zahiri ba.

A cewar hukumomin tsaron dai an kama motar ce a wani wurin binciken ababan hawa a gab da garin Alkaleri, kuma rundunar yansandan jihar ta Bauchi ta ce, yayin da jami'an tsaro na sojoji suka tare motoci suna bincikensu sai mutanen dake cikin motar dake dauke da bama-baman suka yi fitar bargden guza suka shiga daji, kana suka bar motar a wajen tun kafin a zo kansu da bincike, daga bisani kuma jami'an tsaron suka gano makaman a cikinta.

Kakakin rundunar yan sandan jihar ta Bauchi, ASP Hassan Muhammad, ya shida mani ta wayar tarho cewa, makaman da aka gano a cikin motar sun hada da bama-bamai guda goma sha uku nau'I'I daban-daban, da bindigogi kirar AK 47 da zungur-zunguru na albarusai masu yawan gaske, kuma daga bisani an gayyato kwararru kan sha'an bama-bamai suka kwance bama-baman da suran makaman.

A baya-bayan nan dai, ana yawan fusknatar hare-hare na bama-bamai a cibiyoyi daban-daban a Nijeriya musamman a jihoihin arewacin kasar, kuma ana zargin cewa ana jigilar makaman ne tsakanin jihohin kasar, inda a wasu lokuta ma ake zargin jami'an tsaron da rashin gudanar da bincike kan ababawn hawa kamr yadda ya kamata, sabo da karancin na'uorin bincike na zamani, wasu lokutan kuma ana zargin jami'an tsaron da rshin gudanar da binciken baki daya inda suke maida hankali wajen karbar nagoro daga matafiya, lamarin kuma da kansa irin wadanda muggan makamai su wuce salin-alin, in banda katari kan akan yi jefi-jefi, koda shike dai jami'an tsaron kan musanta zargin da ake masu.

Haka nan kuma an sha kama mutane a sassa-daban daban na Nijeriuya na muggan makamai ciki harda bama-bamai, amma daga bisani ba a kara jin duriyar lamarin bayan jami'an tsaron sun bayyana cewa suna gudanar da bincike inda wsu lokutan ma ake zargin cewa akan saki mutanen su ci gaba da wataya cikin kasar, amma da kakakin rundunar yansandan jihar ta Bauchi inda aka yi kamun makaman na baya-bayan nan ya musanta wannan zargi yana mai cewa su jami;an tsaro suna bakin kokarinsu.

A bangare guda kuma a Jihar ta Bauchi, rahotanni daga karamar hukumar Tafawa Balewa na cewa ana ci gaba da fusknat tashin tashina jefi-jefi, inda ko a wayewar garin jihar wasu mutane dab a a iya tantance ko su wane ne ba sun kona gidaje da dama a kauyen Tekman, amma babu hasarar rayuka, inda hukumnomin ke cewa suna ci gaba da bincike.

Karin bayani