Nijer na tafka hasara akan tace man fetur

isoufou Hakkin mallakar hoto
Image caption Shugaban Nijer, Mohammadou Issoufou

A jamhuriyar Nijar kimanin biliyan takwas na kudaden CFA ne matatar garin dan Baki dake jahar Damagaram tayi asara sanadiyar tsaida aikinta da aka yi.

Shugabannin matatar sunce yanzu haka man da ta tace na nan jibge ba a sayar da shi ba, abinda kuma zai kara tsayar da ayyukanta saboda rashin wurin adana man.

Kasar Nijar dai ta fara aikin tace manta ne a ranar 28 ga watan Nuwamban bara.

Masu sharhi akan al'amuran yau da kullum sun bayyana cewar dole ne sai an rage farashin man fetur a Nijer kafin 'yan kasar su koma saya a cikin gida.

Karin bayani