Malaman jami'a sun soma yajin aiki a Ghana

milla Hakkin mallakar hoto bbc
Image caption Shugaban Ghana, John Attah Mills

A Ghana, malaman jami'o'in gwamnati sun shiga yajin aiki na sai abinda hali yayi.

Sun shiga yajin aikin ne suna neman a biyasu kudaden baya wato, 'ariyas' tun daga shekara ta 2010, bayan da aka mayar da su a karkashin wani sabon tsarin albashi - wato Single Spine Salary.

Kwanaki ukun da suka wuce ne su ma malaman kwalejojin koyar da sana'o'i na Polytechnic suka fara nasu yajin aikin.