Karzai ya zargi Amurka akan binciken sojanta

afgan Hakkin mallakar hoto BBCPashto.com
Image caption Shugaba Karzai na tattaunawa da 'yan uwan mamata

Shugaban Afghanistan, Hamid Karzai ya zargi Amurka da kin bada hadin kai wajen bincike akan kisan 'yan kasar goma sha shida da wani soja Amurka ya yi a ranar Lahadin da ta gabata.

Shugaban ya bayyana haka ne bayan taron da yayi da wasu 'yan uwan mutanen da aka kashe.

Mutumin da yayi ta'asar dai an tafi dashi Kuwait kuma ana saran maida shi Amurka don ya fuskanci shari'a a kotun soja.

Al'ummar Afghanistan dai sun nemi a gurfanar da shi gaban kuliya a cikin kasar.

Sakataren tsaron Amurka Leon Panetta wanda ya tattauna da shugabannin Afghanistan a Kabul ya ce akwai damuwa matuka akan irin dabarun warware matsalolin kasar.

Yace: "wannan ne sawu na na shidda a Afghanistan, kuma a ziyara ta ta baya, akwai matukar damuwa akan irin yadda za ayi don cimma yarjejeniya akan makomar kasar."

Karin bayani