Majalisa ta Amince da Kasafin Kudi

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Kasar Najeriya, Good Luck jonathan

Majalisar Dokoki ta Najeriya ta amince da kasafin kudin kasar na bana, wanda ya kai Naira Tirilliyan hudu da biliyan dari takwas.

Kasafin dai ya haura abin da gwamnatin Kasar ta gabatarwa majalisar tun farko na Naira Triliyan hudu da biliyan dari shida.

Majalisar tace ta kara kudaden ne saboda wasu bangarori da ba'a basu hakki sosai ba, kamar kiwon lafiya da noma da kuma samarda ruwan sha.

Haka kuma Majalisar ta kara farashin danyen mai daga dala saba'in kan kowace gangar mai zuwa dala saba'in da biyu, a matsayin maaunin kasafin kudin.

Sai dai irin wadannan kare-karen ne suka haifar da ja-in-ja tsakanin shugaba Goodluck Jonathan da majalisar dokokin a bara; lamarin da ya haifar da karin jinkiri wajen aiwatar da kasafin kudin.

Haka kuma an dai sa tallafin man fetur a cikin kasafin kudin inji yan majalisar, abunda janye shi gaba daya da Shugaban kasar Good luck Jonathan yayi ya jawo zanga zanga da yajin aikin gama ri a kasar.

Karin bayani