Shugaban majami'ar anglican zai yi murabus

Rowan Williams Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban cocin Ingila, Rowan Williams

Shugaban majami'ar Angilan a duniya baki daya, Rowan Williams ya sanar da cewar zai yi murabus daga mukaminsa a karshen wannan shekarar.

Zai koma ne jami'ar Cambrigde inda zai zama shugaban kwalejin Magdalene.

Dr Williams mai shekaru sittin da daya, shine Archbishop na Canterbury wato jagoran addinni a cocin Ingila, kuma ya shafe kusan shekaru goma akan wannan mukami.

Murabus din sa ya zo ne a daidai lokacin da ake samun rashin jituwa a cocin tsakanin masu matsaikanci ra'ayi da kuma masu son abi tsarin al'adun mutanen baya.

Karin bayani