Sojan Amurka na da Ciwo a Kwakwalwa

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojoji a afghanistan

Lauyan sojan Amurkan nan da ake zargin ya kashe 'yan afghanistan su goma sha shida a karshen mako yayi magana da 'yan jaridu a karon farko, inda yace Sojan na da ciwo a kwakwalwarsa.

John Henry Brown, wanda yake kare sojan da har yanzu ba a fadi sunansa ba, ya ce wanda yake karewar ya samu rauni a kwakwalwarsa da ma jikinsa a aiki da yayi a Kasar Iraqi.

An dai dauke sojan da ake zargin zuwa Kasar Kuwaiti daga Sansanin Sojin amurka a Afghanistan.

Mr. Brown, ya bayyana wanda yake karewa a matsayin sojan da ya sha samun yabon girma abun kwaikwayo. Yace yayi magana dashi ta wayar tarho kuma yana shirin ziyaratarsa a Kuwait nan da yan kwnaki kadan.

a cewar Lauyan wannan lamari abun tashin hankali ne ta kowacce fuska, ba wata tantama akai.

"Ina ganin abune da zaa kula ace muna da soja wanda yake da tarihin aiki abun kwaikwayo, sojan da ya sha lambar yabo wanda akaji masa rauni a kwakwalwarsa dama jikinsa kuma duk da haka a aka sake komar dashi aikin. Ina ganin wannan abun a dubane."

Ya nuna damuwa akan yadda sojoji suka tafiyarda alamurran wanda yake karewar, wanda acewar lauyan yana tsoron rashin lafiyartasa.

Rundunar Sojin Amurka dai tace zata fadi sunan sojan ne yayinda aka zayyana tuhume tuhumen da ake masa.

Sai dai yn Afghanistan sunta kiraye kiraye da a gurfanar da Sojan a Kotun kasar abunda hakan nata samu ba.

Karin bayani