Tattaunawar sulhu da 'yan Boko Haram ta ci tura

Hakkin mallakar hoto youtube
Image caption Abubakar Shekau jagoran kungiyar boko haram

A Najeriya, shugaban Majalisar koli ta shari'ar Musulunci ya ce sun janye daga tattaunawar sulhu da suka fara gudanarwa da jami'an gwamnatin kasar da kuma 'yan kungiyar nan ta Jama'atu Ahlis Sunnati Lidda Awati wal Jihad, da aka fi sani da Boko Haram.

A wata sanarwa daya fitar, shugaban Majalisar koli ta shari'ar Musulunci Dr. Ibrahim Datti Ahmad ya ce shi da sakataren majalisar sun yanke shawarar janyewa daga tattaunawar ce saboda sun ga alamar cewa jami'an gwamnatin kasar bada gaske suke ba a tattaunawar da aka fara yi da shugabannin kungiyar ta Boko Haram.

Shugaban Majalisar kolin ya kuma bayyana takaicinsa da yadda bangaren gwamnatin kasar ta ki amfani da wannan damar na baiwa tattaunawr sulhun muhimmanci wanda zai kaiga kawo karshen tashe tashen hankulan da ake fama dasu a kasar.

Sanarwar dai tace ganin irin yadda ake ta fuskantar matsalar tashe tashen hankula a kasar musumman ma a arewacin Najeriyar ne, yasa shugabannin majalisar kolin suka fara lalubo hanyoyin da zasu kaiga kawo karshen tashe tashen hankulan, wadanda ake dangantawa da kungiyar Boko Haram.

Sanarwar ta kara da cewa bayan da 'yan Majalisar koli ta shari'ar Musuluncin suka gudanar da bincike ne, suka gano wani dan jarida a kasar wanda kuma suka tabbatar cewa, ya kan tattauna da shugabannin kungiyar Boko Haram wajen gudanar da ayyukansa a matsayin dan jarida, hakan yasa suka yi amfani da dan jaridar wajen mika sakon neman sulhu ga 'yan kungiyar.

Shugaban Majalisar koli ta shari'ar Musulunci ya kara da cewa, a ranar 5 ga wannan watan ne shi da sakataren Majalisar a madadin sauran mambobin Majalisar kolin, suka tuntubi jami'an gwamnatin kasar don gabatar musu da shawarwarin fara tattaunawa da 'yan kungiyar ta Boko Haram.

To sai dai a cewar sanarwar, bayan da gwamnatin kasar ta umurci wani babban jami'inta ya kasance wakili a tattaunawar tsakanin shugabannin Majalisar kolin da kuma 'yan kungiyar ta Boko Haram, duk wasu batutuwa na sirri da bangarorin suka tattauna da jami'in gwamnati, sai kwatsam suka yaddu a jaridun kasar, abin da cewar Dr Ibrahim Datti Ahmed, shugaban Majalisar koli ta shari'ar Musuluncin, hakan yasa suka fara shakkun cewa ko anya kuwa da gaske gwamnatin kasar take na tattaunawar.

Sai dai wata majiya daga bangaren shugabannin Majalisar kolin ta shari'ar musuluncin tace janyewar da shugabannin Majalisar suka yi a tattaunawar bai rasa nasaba ne da abin da suka fassara a matsayin rashin bada muhimmanci ga tattaunawar daga bangaren gwamnatin kasar, sabannin tattaunawar da a baya gwamnatin Najeriyar ta yi da 'yan kungiyar MENDS masu fafutika a yankin Neja Delta, wadanda a cewar majiyar takanas, gwamnati kan bada jirgin sama a dauko jami'an kungiyar ta MEND zuwa fadar shugaban kasar inda aka tattauna dasu.

BBC tayi kokarin jin martanin gwamnatin Najeriyar kan wannan batu inda an tuntunbi kakakin shugabar kasar Dr Ruben Agbati ta wayar tarho amma bai amsa ba.

Ko a baya lokacin da shugaban Najeriyar Goodluck Jonathan yayi kira da 'yan kungiyar dasu fito su bayyana kansu tare da fayyace bukatunsu domin a tattaunawa da su amma 'yan kungiyar sun yi watsi da kiran saboda a cewarsu, a baya sun turo wani jami'in kungiyar don ya tattauna da jami'an gwamnati, amma aka kame shi.