An halaka mutane goma a Chikun na jihar Kaduna

hari a kaduna

Bayanai daga jihar Kaduna a Arewacin Nigeria na nuna cewa wasu wadanda ba a san ko su wane ne ba sun kai hari a wasu Kauyuka na karamar hukumar Chikun dake kudancin jIhar inda suka hallaka a kalla mutane 10.

Wasu karin mutane biyar kuma sun samu munanan raunuka.

Rahotanni dai sun bayyana cewa wadanda suka rasa rayukkan na su sun hada da limamin wata Majami'a wanda maharan suka harbe bayan sun kone Majami'ar da yake jagoranta.

Tuni dai aka kai wadanda suka sami raunukari zuwa asibitin koyarwa ta jami'ar Ahmadu Bello dake Samaru kusa da Zaria.

Rundunar 'yan sandan jihar ta tabbatar da afkuwar wannan al'amari, inda ta ce ta aike da jami'anta zuwa wannan yanki dake da wahalar zuwa daga babban birnin jihar.

Karin bayani

Labaran BBC