'Yan Libya sun yi murna da kama al-Sanussi

Abdallah al-Sanussi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Abdallah al-Sanussi

Hukumomin Mauritania da gwamnatin Libya sun ce an kama tsohon jagoran hukumar ayyukan sirri na Libya, Abdullah al-Senussi.

Hukumomin Mauratania sun ce an kama el-Senusii ne a filin jirgin saman Nouakchott, babban birnin kasar, bayan da ya isa kasar daga Morocco da fasfo na jabu.

Maurataniya ta ce tana son yin nata binciken kafin ta duba bukatar mika Al Sanussin ga Libya, da Faransa da Kotun hukunta miyagun Laifuka ta Duniya.

Libya ta yi alkawarin yi masa shari'a ta adalci.

A bara ne kotun miyagun laifukan ta fitar da sammacin kama Al Sanussi bisa zargin keta hakkin bil adama a lokacin bore a Libyar na kokarin hambarar da Kanar Gaddafi.

Faransa tana nemansa ne bisa dana bom a jirgin saman fasinja na Faransar 1989, inda dukkan wadanda ke ciki suka mutu, ciki har da Faransawa hamsin da hudu.

Tuni dai aka yi masa shari'ar bayan ido aka kuma same shi da laifi a kan wannan tuhuma.

Karin bayani