Zanga zangar nuna kyamar fyade a Morocco

Zanga zanga a Morocco Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga zanga a Morocco

Masu rajin kare hakkin bilAdama a kasar Morocco sun kira wata zanga zanga a yau, don bayyana adawarsu ga dokar kasar kan fyade.

Dokar dai ta tanadi cewa wadanda suka aikata fyaden su auri wadanda suka yiwa fyade don kaucewa tuhuma.

Kiran na zuwa ne bayan mako guda da wata yarinya 'yar shekaru goma sha shidda ta halaka kanta a arewacin kasar.

Kotu dai ta tilasta mata ne da ta auri mutumin da ya yi mata fyaden, kuma shi da yan uwansa suka rika azabtar da ita.

Rahotannin da suka fito bayan da ta kashe kanta a karshen makon jiya, na nuna cewa mutumin da ya aure ta ya lakada mata duka, wanda masu rajin kare hakkin bilAdama suka rika watsawa ta kafofin sada zumunta na Twitter da Facebook.

Mahaifiyar ta wato Zohra Filali cikin hawaye ta bayyana bakin cikinta game abinda ya faru ga yar ta a gaban kabarinta.

Shugabar kungiyar masu kare hakkin mata a Morocco wato Democratic League for Women's Rights in Morocco, Fouzia Assouli, ta shaidawa BBC cewa doka mai lamba 475, abin kunya ce, kuma ta yi kira ga gwamnatin kasar da ta jingine ta.

Karin bayani