Ana taron girmama gawar Paparoman Kibdawa

Gawar Paparoman Kibdawa na kasar Masar Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gawar Paparoman Kibdawa na kasar Masar

Kiristoci Kibdawa suna can sun taru a cocin Catheral ta St Mark a birnin Alkahira, don nuna ban girma ga gawar Paparoman Kibdawan na kasar Masar, Shenouda na Ukku na Iskandariya.

A jiya Asabar ne Paparoman Kibdawan ya rasu yana da shekaru tamanin da takawas a duniya.

Gawar, wadda aka dora a kan karagar mulkin Paparoman Kibdawan, an saka mata tufafin paparomancin, kuma za ta ci gaba da kasancewa ne a nan tszwon kwanaki ukku, zuwa ranar da za a yi janazarsa.

Karin bayani