Yan adawa a Cuba sun shiga hannun jamian tsaro

Masu zanga zanga a Cuba Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Masu zanga zanga a Cuba

Yan sanda a kasar Cuba sun cafke yan adawa da dama wadanda ke zanga zanga na mako mako, ana saura mako guda shugaban darikar Katolika Paparoma Benedict ya kai ziyara tsibirin.

An kama jagorar yan adawa ta Kungiyar Ladies in White da sauran wasu mutanen fiye da talatin a lokacin da suke kan hanyar su ta zuwa wani taron addu'a a safiyar ranar Lahadi.

Yan sandan sun kuma kame wasu masu macin ne a lokacin da suka yi kokarin zarce inda suka saba yin macin, wanda jamian tsaro ke barinsu..

Matan masu ilmin kasar ne da yan jarida, da masu rajin kare hakkin bilAdama ne suka kafa kungiyar ta Damas de Blanco a shekarar 2003, lokacinda aka kama wasu bijirarrun yan adawa.

Tuni dai aka sako mutanen, bayanda mujamiar Katolika ta shiga tsakani.

Karin bayani

Labaran BBC