Shugaba Sarkozy ya yi allawadai da kisan wasu yara

Shugaba Sarkozy na Faransa Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Sarkozy na Faransa

Wani dan bindiga ya kashe yara kana uku da kuma wani malami a wata makarantar Yahudawa dake birnin Toulouse a kudancin Faransa.

Yanzu haka dai akwai wani yaro da lamarin ya shafa yana cikin wani hali.

Wani mai gabatar da kara Micheal Valet yace maharin ya bi yaran ne da gudu cikin makarantar yayin da su kuma suke gudu.

Rahotanni dai sunce ya tsere ne akan wani babur.

Yayinda yake magana a wurin da lamarin ya abku shugaban kasar Faransar Nicolas Sarkozy yayi Allah Wadai da harin,inda yayi alkawarin hukunta duk wanda aka kama da aikatawa.

'Yan sanda dai na danganta wannan harbi da irinsa da ya auku a makon da ya gabata inda aka kashe soja uku.

Karin bayani