Amnesty ta zargi NATO da kashe fararen hula a Libya

kungiyar Amnesty International Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption kungiyar Amnesty International

Kungiyar kare hakkin bilAdama ta Amnesty International ta yi kakkausar suka ga kungiyar kawance ta NATO bisa halaka mutane fiye da hamsin sailin da take ruwan bama bamai a Libya yau shekara guda kenan.

A wani rahoto da ta fitar bayan shekara guda da kaddamar da hare hare ta sama da kungiyar NATO ta yi a Libya, Amnesty ta ce hare haren ta sama da Majalisar Dinkin Duniya ta amince NATO ta yi, don kare fararen hula ne ba halaka su ba.

Amnesty ta ce NATO ta ki gudanar da bincike game da musabbabin mutuwar fararen hulan sakamakon ruwan bama baman.

Wasu dai sun zargi NATO da kasancewa dakarun sama na yan tawayen Libya wanda ya kai ga hambarar da gwamnatin Kanar Gaddafi.

Watanni biyar bayan rasuwar kanar Gaddafi, har yanzu Libya na cikin rikici.

Yawancin yan Libya, musamman yan yankin Gabashin kasar a Bengazi, na ganin hare haren da kungiyar NATO ta kai a matsayin wanda ya yi gagarumar nasara, wanda kuma ya kai ga ceto rayukan dubun dubatan fararen hula daga dakarun kanar Gaddafi, kuma an shirya gudanar da bukukuwa a wasu biranen kasar.

Karin bayani

Labaran BBC