Yara da dama na fama da yunwa a Nijar

Tamowa a Niger Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Matsalar tamowa a Nijar na kara kamari

Matsalar karancin abinci da jamhuriyar Nijar ke fuskanta tana haddasa matsalar tamowa ga kananan yaran kasar.

A yanzu haka asibitin garin sabon mashi ya fara cika makil da yara musamman a ranakun da ake raba masu abinci.

Bayanan da malaman asibitin suka bayar sun ambato cewa asibitin na karbar sama da yara dari masu tamowa ko wacce safiya.

Bayanai daga hukumomin asibitin Maradin dai na nuna cewa, yaran da ake kaiwa don kula da su sakamakon matsalar tamowa, sun zarta wadanda ake kaiwa a bara.

Karin bayani