Mun rufe kofar tattaunawa da gwamnati - Boko Haram

Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau

Kungiyar jama'atu Ahlussunah lidda'awati wal jihad da aka fi sani da suna, Boko Haram a Najeriya, ta ce a yanzu ta rufe kofar duk wata tattaunawa da gwamnatin kasar domin a ganinsu ba da gaske gwamnatin take ba.

Kungiyar ta kuma tabbatar da cewa, da yawunta majalisar kula da al'amuran shari'a a Najeriya ta fara tattaunawa da gwamnatin Najeriya, tattaunawar da ta rushe a karshen makon da ya gabata.

Wani dake ikirarin magana da yawun kungiyar da ake wa lakabi da Abu Qaqa ne ya bayyana haka a hira da manema labarai a birnin Maiduguri.

Mai magana da yawun kungiyar ta Boko Haram ya ce sun ga ya wajaba ne su yi wannan karin bayani, ganin cewa batun tattauanawar su da gwamnatin tarayya ya mamaye kafofin yada labarai a 'yan kwanakin nan.

Abu Qaqa ya ce, sun amsa kiran da Dr Datti Ahmad, shugaban majalisar kula da al'amuran shari'ar Musulunci a Najeriya ya yi musu na a tattauna ne, saboda suna ganin kimar sa, amma tun asali suna da shakku akan ko da gaske gwamnati take kan batun tattaunawar.

Mai magana da yawun kungiyar Boko Haram din ya ce, ba da jimawa bane shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya yi kira ga kungiyarsu da ta fito a tattauna da su, su kuma bayyana bukatunsu, bukatun da ya ce sun bayyana wadanda suka kunshi sako musu dukkan 'yan kungiyar su da aka kama ba tare da gindaya wani sharadi ba.

'Abin kaico ne'

Ya ce an fara ganawa tsakaninsu da gwamnati, amma gwamnati ta sa aka kama daya daga cikin 'ya'yan kungiyar Abu Darda wanda suka tura ya wakilce su.

Kuma tun daga lokacin suka ga cewa ba za su iya sake amincewa da gwmanatin Najeriya ba.

Sai dai sakamakon rokonsu da wasu muhimman 'yan Najeriya da suke matukar girmamawa suka yi, sun amince su tattauna, amma abin kaico ne ganin an bata shirin tun bai je ko ina ba.

Image caption Hoton Harin bom da ya hallaka wani dan sanda a Kadunan Najeriya

A don haka Abu Qaqa ya ce ba za su kara saurarar duk wasu da suka ce su zo su sasanta su da gwamnati ba, don haka jami'an tsaron gwamnati su yi duk abinda suka ga za su iya, su ma za su maida martani da tasu iyawar.

Dangane da wani dan jarida da ya yi ikirarin ana barazana ga rayuwar sa kuwa, mai magana da yawun kungiyar ta Boko haram ya ce, dan jaridar shi ne silar hada su da kwamitin Dr Datti Ahmed, a don haka suna shawartarsa da sauran 'yan jaridu da kada su razana da duk wata barzana.

A karshen makon da ya gabata ne shugaban Majalisar kula da al'amuran shari'ar musulunci a Najeriya Dr Datti Ahmad ya fitar da wata sanarwar da a cikinta ya ce ya janye daga tattaunawar da suke kokarin kullawa tsakanin gwamnati da kungiyar Boko Haram, saboda in ji shi, suna zargin bangaren gwamnati da tseguntawa 'yan jaridu batutuwan da ake tattaunawa cikin sirri.