An fara farautar wanda ya kai hari a Faransa

Harin Faransa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Harin Faransa

Za a fara daya daga cikin farautar mutane mafi girma cikin shekarun baya bayan nan a kasar Faransa don gano mutumin da yayi kashe kashen Toulouse na kasar Faransa.

Yan siyasa da yan sanda sun yi gargadi game yada jita jitar musabbabin yin wannan kashe kashe.

Yan sanda sun danganta harbe-harben bindigar da wasu hare-hare biyu da aka kai wannan yankin a makon da ya wuce lokacinda aka kashe wasu sojoji ukku.

Sojoji ukkun da ya halaka dai, dukkaninsu yan asalin yankin Arewacin nahiyar Afirka ne, wanda kuma ya sa wasu ke zargin cewa, makashin na kiyayya ne ga dukkanin tsiraru a kasar, wato Musulmai da Yahudawa.