An fara farautar wanda ya kai hari a Faransa

Harin Faransa Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Harin Faransa

Hotunan bidiyon da aka samu daga kamarorin tsaro sun nuna yadda aka kashe yara uku da wani malamin makaranta a Toulouse a ranar Litinin ciki hadda kisan wata yarinya 'yar shekara bakwai.

Hoton bidiyon ya nuna yadda dan bindigan ya jaa gashin Miriam Monsonego kafin ya harbeta.

Ministan harkokin cikin gidan Faransa, Claude Giuean ya ce dan bindigar ya rike abin daukar hoton bidiyo a lokacin da yayi kisan.

Wani mai shago a Toulouse inda aka yi ta'asar, ya ce a yanzu sun tsaurara matakan tsaro a shagunansu.

Ya ce,suna duba jakunkunan mutane tare da maida hankali akan masu shigowa.

Haka kuma suna sa ido sosai a kan wadanda ke shigowa cikin shago.

Mai shagon ya ce suna cikin tsoro i saboda akwai wani mamuguncin dake zaune a Toulouse.

Tuni dai aka dauki gawarwakin wadanda aka kashen zuwa Israila don biznewa.