An kashe mutane 40 a hare hare a Iraki

iraki Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Mutane 40 ne suka mutu

An kai hare haren bam a birane daban daban na kasar Iraki, inda akalla mutane arba'in da biyar suka rasu sannan wasu da dama suka jikkata.

Hari mafi muni shine wanda aka kai a birnin Karbala na 'yan Shi'a, inda hukumomi suka ce mutane 13 ne suka rasu.

Kakakin jami'ar 'yan Shi'a, Haider Al-Abadi ya ce watakila a cigaba da samun wasu karin hare haren, a nan gaba.

Yace "Abun takaici lokacin da aka turawa suka mamaye Iraki, kasar ta zama wata cibiyar 'yan ta'adda da kuma Al Qaida. An horadda dasu a Iraki kuma suna son nuna cewar demokradiya bata aiki a kasar".

An kai wani harin a Kirkuk da kuma babban birni kasar wato Bagadaza, inda aka samu fashewar wani wanu kusada ma'aikatar harkokin wajen kasar.

Kawo yanzu dai babu kungiyar data dauki alhakin kai hare haren.

Karin bayani