Jihohin Nigeria za su amfana da 13 cikin dari na kudaden maadinai

nigeria
Image caption nigeria

Gwamnatin Nigeria ta ce jihohin kasar dake da arzikin ma'adanai za su fara amfana da kashi 13 cikin dari na kudaden shigar da suka samar ta hanyar sayar da ma'adinai.

Hukumomin Nigeriar dai sun ce hakan wani yunkuri ne na zaburar da jihohin wajen farfado da ayyukan hakar ma'adanai maimakon dogaro da man fetur.

Kafin wannan lokaci dai jihohi tara ne kadai masu arzikin man fetur dake kudancin kasar ke amfana da wannan kaso da yawansa ya kai dubban miliyoyin naira.

To saidai masana a kasar na ganin cewa, ba wai rashin kudi ne ke damun wasu yankunan kasar ba, musamman ma dai Arewacin kasar, illa rashin gudanar da aiyukan ci gada da kudaden da ake samu.