'Yan adawan Syria suna cin zarafin bil adama

syria Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin adawa a Syria

Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce wasu daga cikin 'yan adawa a Syria sun ci zarafin bil adama, ciki hadda yin garkuwa da mutane don karbar kudin fansa, da azabtar da mutane da kuma kashesu.

Kungiyar ta ce irin ta'asar da sojojin gwamnati suka aikata, ba wata dama ce ga 'yan adawa su aikata laifi ba.

Human Rights Watch ta ce wasu kungiyoyin dake adawa da gwamnati sunyi hakane watakila bisa umurnin majalisar 'yan adawar Syria.

Kungiyar ta yi kira ga shugabannin adawa a Syria sun fito suyi Allah wadai akan irin wannan ta'asar.

Karin bayani