An tabbatar da kama Agaly Alambo a Nijar

Aghaly Alambo Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Aghaly Alambo

A jamhuriyar Nijar hukumomin shari'ar kasar sun kama madugun tsohuwar kungiyar tawayen MNJ, kuma mashawarci a fadar shugaban majalisar dokokin kasar, Malam Agaly Alambo.

Rahotanni na cewa ana zarginsa ne da hannu a fataucin makamai da ma hada baki da wasu mutane domin aikata ta'addanci .

Sai dai ya zuwa yanzu gwamnatin kasar ta Nijar ba ta yi wani karin haske a kan kamun na Agaly Alambon ba.

A baya an zargi Agali Alambo da taka muhimmiyar rawa wajen kai wadanda aka rika zargi sojojin haya ne zuwa Libya, domin fada a bangaren tsohuwar gwamnatin marigayi kanar Gaddafi.

Kamun da aka yi wani da ake zargin yana fasakwaurin makamai a jamhuriyar Nijar din a bara, shi ake hasashen ya kai ga cafke Agaly Alambo yanzu.

Karin bayani