'Yan sanda sun killace gidan dan bindiga

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption yan uwan wadanda aka kashe a Faransa na daukar gawawwakin

Masu shigar da kara a Faransa, sun ce dan kasar da ya kai wasu jerin hare-hare a yankin Toulouse na da muradin kai karin wasu hare-haren.

Babban jami'in yaki da ta'addanci Francois Molins ya ce mutumin da ake zargi mai suna Mohammed Merah mai shekaru 23 dan asalin kasar Aljeriya, ya yi aniyar kashe wani soja da 'yan sanda biyu.

Ana zargin Merah wanda ya ce ya samu horo daga Alqaeda, da kisan sojoji uku da kuma Yahudawa hudu.

Jami'an 'yan sandan kasar na ci gaba da killace gidan da dan bindigan ke ciki.

Tun da farko dai an kai mahaifiyarsa wajen da nufin sanya shi ya mika wuya.

Ranar Litinin din da ta gabata ne wani dan bindiga ya harbi wani malamin Addinin Yahudu da yayansa guda biyu, dan shekara hudu da dan shekara biyar da kuma wata yarinya 'yar shekara bakwai a wajen wata makarantar Yahudawa a Faransa.

A yau ne kuma aka binne wadanda aka kashe su hudu a harin, inda Ministan harkokin wajen faransa, Alain Juppe ya raka gawarwakin daga Faransa zuwa Birnin Kudus.

Jami'an 'yan sanda dai na tunanin cewa wanda ya yi wannan kisan ne ya kashe sojojin Faransa guda uku a yankin a farkon wannan watan, kuma akwai yiwuwar ya sake aikata laifin kisan.

A wani bikin bankwana a filin jiragen sama na Paris, Shugaban kasar ta Faransa Nicolas Sarkozy ya ce iyalan mamatan sun nuna jaruntaka.

Mazauna yankin da aka yi kisan sun shiga fargaba da alhini tun ranar Litinin din da ta gabata.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service