An kai hari kusada fadar shehun Borno

maiduguri Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wani hari a Maiduguri

Rahotanni daga Maiduguri babban birnin jihar Borno sun ce dazu ne wasu 'yan bindiga suka kai hari a wasu unguwanni dake tsakiyar birnin, ciki har da unguwar Shehuri inda suka budewa wasu jami'an tsaro dake a kusa da fadar Mai Martaba Shehun Bornon, wuta.

Wadanda suka ga lamarin sun ce sun ga gawawwakin wasu 'yan sanda uku yayin da kuma jama'a da dama suka rika ruguguwar tserewa zuwa gidajensu .

Rundunar 'yan sandan jihar Borno ta tabbatar da aukuwar lamarin, sai dai ba ta ce an samu asarar rayuka ko kuma jikkata ba.