Sabon tsarin zaman lafiya a Syria

assad Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaba Assad da Mista Kofi Annan

Bayan shafe makonni ana sasantawa don samo hanyoyin kawo karshen zubar da jini a Syria, kwamitin tsaro na majalisar dinkin duniya da gaggarumin rinjaye, ya amince da shirin samar da zaman lafiya da wakili na musamman Kofi Annan ya gabatar.

Kwamitin tsaron ya bukaci gwamnatin Syria da 'yan adawa su zartar da shawarwarin Mista Annan ba tare da bata lokaci ba.

Wasu daga cikin shawarwarin sun hada da bada damar kai kaya agaji, da kuma janye dakarun gwamnati daga birane da garuruwa.

Sakatariyar harkokin wajen Amurka, Hillary Clinton ta gargadi shugaba Assad ya zartar da matakan ko kuma ya fuskanci matsin lamba.

A baya dai Rasha da China sun hau kujerar naki a yinkurin zartar da wani kuduri na majalisar dinkin duniya akan Syriar.