Hukumomi sun dukufa kan yakar shan inna a Najeriya

Hakkin mallakar hoto ap
Image caption ana digawa yaro allurar polio

Kungiyoyi da hukumomi masu ruwa da tsaki a yaki da cutar polio a Najeriya, sun bullo da wani shiri na samar da masu wayar da kan jama'a a yankunan da cutar tafi kamari.

Sabon shirin dai, na daga tsare- tsare na gaggawa da masu ruwa da tsakin suka fito da shi a Najeriya, wanda ake fatan zai taimaka wajen rage yawan yaran da ake tsallakewa yayin digon maganin rigakafin cutar.

A cikin shirin dai jamian, za su bi gida- gida don gamsar da iyaye su bari a yiwa 'ya'yansu digon rigakafin allurar cutar ta shan inna.

Tsarin dai wanda aka fito da shi na da hadin gwiwar hukomomin samar da lafiya a matakin farko ta Najeriya, da kuma Kungiyoyi da suka hada da asusun Bill da Milinda Gates, da asusun tallafawa yara na Majalisar Dinkin Duniya da kuma cibiyar yaki da cututtuka gami da rigakafi ta kasa da kasa.

Dukkaninsu za su hada karfi da karfe don tunkarar jihohin da cutar tafi kamari da suka hada da Kebbi da Sakkwato da Zamfara da Katsina da Kano da Jigawa da Borno da kuma Yobe.

Karin bayani