Mutumin da 'yan sanda ke nema a Faransa ya mutu

Faransa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yan sanda sun killace gidan tun ranar Laraba da daddare

Ministan cikin gida na kasar Faransa ya ce dan bindigar da aka zarga da kisan mutane bakwai a birnin Toulouse, ya mutu bayan ya fado daga tagar gidansa bayan da 'yan sanda suka yiwa gidan kawanya.

'Yan sanda sun shiga gidan da Mohammed Merah ya ke bayan kawanyar da aka yiwa gidan sama da kwana guda.

Sai dai rahotanni sun ce wanda ake zargin ya mutu ne bayan da ya fado ta tagar gidan nasa tare da wata bindiga a hannunsa - ya kuma harbin 'yan sandan.

Akalla jami'an 'yan sanda biyu ne suka jikkata a lamarin.

Merah, dan shekaru 23, an zarge shi da kisan mutane bakwai a wasu hare-hare daban-daban guda uku.

Tun da farko ministan cikin gida Claude Gueant na Faransa ya ce Merah ya so ya mutu "tare da makamai a hannunsa" kuma an kasa yin magana da shi cikin dare.

Kafin a kaddamar da harin, Mr Gueant ya ce a bayyana take cewa Merah yana nan da ransa.

Sai dai 'yan sanda sun fuskanci turjiya tun bayan da suka kaddamar da farmakin da misalin karfe 9:30 na daren ranar Alhamis.

Karin bayani