Sojoji sun yi juyin mulki a Mali

Juyin mulki a Mali Hakkin mallakar hoto AFP

Sojojin da suka yi bore a Mali sun ce sun kawo karshen mulkin Shugaba Amadou Toure, sannan kuma sun dakatar da kundin tsarin mulkin Kasar da kuma sauran hukumomin gwamnati.

Ba a ji komai ba daga bangaren shugaban kasar ba kawo yanzu.

Shugaban rundunar sojojin da suka yi boren kyaptin Amadou Sanogo ya bada sanarwar sanya dokar hana hana zurga zurga a gidan talabijin din kasar.

Ikirarinsu na kwace ragamar ikon kasar na zuwa ne bayan kiraye-kiraye daga kasashen duniya na a kwantar da hankali game tashin hankalin da ya barke na baya- bayan nan a kasar, inda aka samu rahotannin harbe- harben bindigogi a babban birnin Kasar Bamako.

Kafin juyin mulkin dai kakakin rundunar soji na Mali ya bayyana harin Sojojin da suka yi boren a matsayin yunkurin juyin mulki.

Sojojin da suka juya baya kuma suka bada sanarwar juyin mulki tun farko sun mamaye gidan Talabijin na kasar, sun kuma bude wuta kan dakarun sojin da ke gadin fadar shugaban kasar kafin su bada sanarwar juyin mulkin.

Sojin da suka yi bore dai sun ce basu da makamai da kayan aikin soji da za su yaki 'yan tawaye a Arewacin Sahara.

Wannan duka na zuwa ne kasa da wata daya kafin a gudanarda zaben shugaban kasar da a baya aka shirya a kasar, rashin gamsuwa ya karu kan yadda tsohowar gwamnatin ta tafiyar da rikici a arewaci.

Hambararren shugaban kasar, Amadou Toumani Toure, kafin sanarwar juyin mulkin; ya lashi takobin zai gudanar da zaben ba tare da bata lokaci ba duk kuwa da rikicin.

Karin bayani