Mutane miliyan 15 na bukatar agajin abinci

Yara masu fuskantar karancin abinci mai gina jiki Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yara masu fuskantar karancin abinci mai gina jiki

Akalla mutane miliyan goma sha biyar ne aka kiyasta cewa suna bukatar karancin abinci a yankin Sahel na nahiyar Afrika.

Miliyan shida da rabi daga cikin wannan adadi sun fito ne daga jamhuriyar Nijar.

Daraktan Asusun Unicef a Nijar y a ce kimanin yara 40,000 ke fuskantar matsalar yunwa a kasar.

“Akwai fargabar kara samun yaran da za su fuskanci matsalar yunwa idan ba a dauki mataki ba”, a cewar Unicef.

Jama’a sun yi kaura

Shi ma gwamnan jihar Telebiri ya shaida wa BBC cewa kusan rabin kauyukan yankin na fama da matsalar karancin abinci.

Kungiyoyin agaji sun ce ana bukatar kimanin saifa biliyan 180, kwatankwacin dalar Amurka miliyan 362 domin ciyar da jama’a.

Amma suka ce kimanin kashi talatin cikin dari ne kawai na wannan adadi aka sa mu kawo yanzu.

Wakiliyar BBC Aichatou Moussa wacce ke ziyartar jamhuriyar ta Nijar, ta ce mutane na matukar bukatar tallafin abinci – inda suka yi kaura kuma suke zaune a cikin bukkoki.

Da dama daga cikin wadannan mutane sun yo kaura ne domin abinci, inda suke yin ayyuka daban-daban domin samun abinci.

'Mutane na tafiya da kyar'

Wasu daga cikin magidantan da BBC ta zanta da su, sun ce abinda suke samu baya isarsu ciyar da kawunansu da kuma iayalansu.

“Mun ga mutane suna tafiya da kyar domin neman dan abincin da za su sanya abaka a jihar Maradi”, a cewar wakiliyarta mu.

Lamarin dai ya fi shafar yankin Telebiri da Arewacin kasar ta Nijar, a cewar mahukunta.

Sai dai anata bangaren gwamnati ta ce tana iya kokarinta wurin tallafawa jama’ar da ke fama da karancin abincin.

Rashin kyawun damina da hauhawar farashin kayan abinci su ne suka haifar da karancin abincin da jama’ar kasar ke fama da shi.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service