Rashin tsaro na barazana ga ayyukan agaji

Yankin Sahel
Image caption Mummunan fari na daga cikin abubuwan da suka haifar da karancin abinci

Rashin tsaro da tabbas na siyasa na kawo cikas ga ayyukan agaji da kuma kara kazanta matsalar karancin abincin da dubun-dubatar jama'a ke fama da shi a yankin Sahel.

Baya ga dimbin mutanen da ke fama da tamowa a jamhuriyar Nijar - wadanda tuni kungiyoyin agaji suka ce yana neman gagarar kundila.

Akwai kuma dubban jama'a da suka tserewa rikicin da ake fama da shi a Arewacin Mali zuwa kasashen Nijar da Mouritania da Burkina Faso da kuma wasu sassan Chadi.

Mutane 130,000 da aka kiyasta sun tsere sakamakon rikicin sun kai kashi 0.8% cikin dari na baki dayan jama'ar Mali.

Wani mai magana da yawun Majalisar Dinkin Duniya Adrian Edwards ya yi gargadin cewa suna cikin "matukar bukatar" kayan abinci - ciki harda matsuguni da abinci da ruwan sha da kuma magunguna.

An hana Red Cross kai kayan agaji

Wasu da ake zargin 'yan tawayen Abzinawa ne a Arewacin Mali sun hana kungiyar agaji ta Red Cross shiga yankin, bayan da suka yaga tutarta a lokacin da ta yi kokarin isa yankin Tessalit.

Yankin na Tessalit na hannun 'yan tawaye ne bayan da suka kwace shi sakamakon fadan da suka gwabza da dakarun gwamnati.

"Yan bindiga sun hana tawagarmu da ke kan hanyar zuwa Tessalit shiga yankin, a don haka sun koma Gao," a cewar wata majiya ta ICRC.

"Manufarmu ita ce mu kai dauki ga fararen hula," a cewar majiyar wacce bata so a ambace ta ba.

'Yan tawayen na Mali dai na bukatar kafa tsarin shari'ar Musulunci ne a Arewacin kasar, kamar yadda wani jagoransu ya bayyana a wani faifan bidiyo da kamfanin dillancin labarai na AFP ya gani.

'Yawancin 'yan tawayen Abzinawan sun dawo ne daga kasar Libya inda suka gwabza yaki a bangaren tsohon shugabnan Libya Kanal Gaddafi - sannan suka sake kaddamar da aniyarsu ta nemanwa yankin na su 'yanci.

Hakkin mallakar hoto
Image caption Dubban mata da kananan yara ne ke bukatar agaji

Mali da kasar Nijar mai makwaftaka da ita sun fuskanci irin wannan boren a shekarun 1960 da 1990 da farkon shekara ta 2000, sannan lamarin ya sake bulla tsakanin 2006 da 2009.

Juyin mulki a Mali

Wani abu da zai kara kawo cikas ga ayyukan agajin shi ne juyin mulkin da aka yi a kasar Mali - da kuma alwashin da 'yan tawaye suka dauka na ci gaba da yakin da suke yi.

Kasar Nijar wacce ta fi fuskantar 'yan gudun hijirar na Mali, tana fama da nata matsalolin.

Wasu alkaluma da malaman asibiti suka fitar sun ce matsalar karancin abinci da jamhuriyar Nijar ke fuskanta tana haddasa matsalar tamowa ga kananan yaran kasar.

Bayanai sun ce asibitin na karbar sama da yara dari masu tamowa ko wacce safiya.

Hukumomi a asibitin Maradi sun ce yaran da ake kaiwa don kula da su sakamakon matsalar tamowa, sun zarta wadanda ake kaiwa a bara.

Karin bayani