Za'a fara shari'ar Shell da 'yan Niger Delta

Irin gurbata muhalli da malalar mai ke yi a Najeriya Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Irin gurbata muhalli da malalar mai ke yi a Najeriya

Lauyoyin dake kare 'yan Najeriya fiye da dubu goma sha daya za su soma shari'a da Kamfanin mai na Shell a birnin London.

A bara ne dai kamfanin Shell ya amince yana da alhakin malalar mai da aka samu a yankin Niger Delta a shekarar 2008 da kuma shekarar 2009.

Wakilan al'ummar Bodo a yankin na Niger Deltan, sunce sun garzaya kotu ne domin samun cikakkiyar diyyar da suke bukata saboda lalata musu muhalli da aka yi.

Wakilin BBC yace lauyoyin mutanen sun ce tattaunawar su da Kamfanin Shell ta cije a makon daya gabata, saboda haka tafiya kotu, ita ce suke gani a matsayin mafita.