Amurka ta tuhumi sojanta da kisa a Afghanistan

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Hoton Robert Bales da ake tuhuma

Jami'ai a Amurka sun ce zasu tuhumi sojan nan Ba'amurke da ake zargi da kashe 'yan Afghanistan.

Jami'an dai sun ce Sergeant Robert Bales, zai fuskanci tuhume- tuhume na zargin kisa goma sha bakwai da kuma wasu karin tuhumar guda shida na yunkurin aikata kisa.

An zarge shi da kashe yara tara da manya takwas a gidajensu a wasu kauyuka guda biyu dake kudancin Afghanistan.

Kisan dai ya jawo zanga-zanga mai zafi a kasar Afghanistan.

Ana zargin Sergeant Robert Bales da kashe yara tara da manya takwas yayinda suke barci a gidajensu.

An kama shi ne jim kadan bayan kisan a Afghanistan, bayanda ya mika kansa.

Rundunar sojin Amurka dai ta dauke shi zuwa kasar Kuwait kafin a dawo da shi Amurka.

A halin yanzu dai ana tsare da shi a kurkukun soji a Fort Levenworth dake Kansas.

Tun farko dai dauke Sergeant Robert daga kasar Afghanistan bai yiwa 'yan kasar da dama dadi ba, inda suka yi kiraye-kiraye cewa a gurfanar da shi a gaban kotu a Afghanistan din.

Lauyan wanda ake tuhumar John Henry Browne ya ce wanda yake karewa yana da rauni a kwakwalwarsa da kuma damuwa ta iyali.

Za a zuba ido a ga yadda shari'ar sojan dan Amurkan za ta kaya.