PDP ta shiga rudani a arewa maso gabas

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaban Kasar Najeriya, Goodluck Jonathan

A Najeriya wata sabuwar kura ta dabaibaye jam'iyyar PDP mai mulkin kasar bayan taronta na yankin Arewa maso Gabashin kasar.

Shuwagabannin jam'iyyar sun sanar da sunan mutumin da zasu mika wa uwar jam'iyyar ta kasa a matsayin shugaban jam'iyyar na kasa.

Bayan taron jam'iyyar na shiyya da aka gudanar a garin Bauchi, reshen Jam'iyyar na Arewa maso gabashin Najeriyar ya bayyana cewa sun zabi Dokta Musa Babayo a matsayin wanda za' a mika sunansa ga uwar jam'iyyar.

To sai dai kuma wasu yan Takarkarun da suke neman wannan kujerar a Yankin na ganin ba ayi musu adalci ba kuma ba zabe a aka gudanarba.

Alhaji Bamanga Tukur wanda shima ke neman shugabancin jam'iyyar daga yankin na Arewa maso gabashi, ya ce ba zabe aka yi ba, kuma shi yana kan bakansa na yin takara a babban taron jam'iyyar na kasa da za a yi a ranar Asabar mai zuwa.

Tun farko dai ana wa bamanga Tukur kallon dan takarar da Shugaba Good Luck ke marawa baya, sai dai mai bawa Shugaban Kasar Good Luck Shawara ta fannin siyasa, Dr Ahmed Gulak ya shaidawa BBC cewa babu wanda shugaban kasar ya ce dan takararsa ne.

Da dukkan alamu dai zaa fafata a Ranar asabar din da zaayi babban taron Jamiyyar kan wanda zai dane kujerar karagar mulkin Jamiyyar mai mulki.

Karin bayani