Jami'yya mai mulki a Najeriya za tayi zabe a yau

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Shugaba Jonathan

A yau ne Jam'iyyar PDP za ta gudanar da babban taron ta na kasa baki daya, inda za tayi zaben shugabannin ta na Kasar.

'Yan takara fiye da goma ne ke gwagwarmayar neman darewa kujerar shugabancin jam'iyyar, mukamin da aka ware wa shiyyar arewa maso gabashin kasar.

an dai shafe mako guda ana dambarwa tsakanin dan takarar da ake zargin shugaba Goodluck Jonathan ke marawa baya, da kuma wanda ake zargin gwamnonin yankin ke marawa baya.

Jamiyyar dai a yankin arewa maso gabacin kasar ta zayyana wanda ta ce za ta bada sunansa a matsayin wanda take son ya zama shugaba inda wasu yan takarar suka ce basu lamunta.

Sai dai akwai yiwuwar wasu yan takarar za su hada karfi waje guda don yakar musamman wanda Jamiyyar ta yankin ta ce shine zai zama shugaban Jam'iyyar.

Ana saran Jam'iyyar mai mulki a Najeriya da tayi kaka gida a siyasar kasar za ta samu sabon shugaba.

Karin bayani