Tarayyar Turai ta kara saka wa Syria takunkumi

Shugaba Assad da matarsa Asma Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaba Assad da matarsa Asma

Hukumomi a Brussels sun ce ministocin kasashen tarrayar Turai sun amince a kan sababbbin takunkumi a kan Syria, ciki har da haramtawa matar shugaba Assad, Asma , da kuma wasu iyalan gidan shiga cikin kasashen Turai.

Sabbin matakan da aka dauka, sun hada da hana iyalan taba kaddarorinsu na Turai abinda ake gani zai shafi makusantan shugaba Assad har su 12.

Ministan harkokin wajen Sweden, Carl Bildt ya ce, idan aka saka takunkumin, tabbas abin zai shafi wasu bangarorin tattalin arzikin kasar ammai shugabanni a kasar sun san yadda za su yi su ci gaba da rayuwarsu irin ta kawa.

Sai dai ya ce za su ci gaba da matsa musu lamba.

Sai dai kuma hukumar kula da shige da fice ta Birtaniya ta ce ba za a iya hana Asma matar shugaba Assad shiga Birtaniya ba, saboda ita yar kasar ce.

Karin bayani