Paparoma Benedict ya isa Mexico

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Pope Benedict

Paparoma Benedict ya isa Mexico, a farkon ziyarsa ta aiki zuwa Kasar tun lokacin da ya zama Paparoma, daga nan zai isa kasar Cuba .

Yayin ziyarar tasa zuwa Mexico, Paparoma, zai tattauna da shugaban kasar Felipe Calderon, kuma zai bayyana ga dimbin mabiya da suka kai kusan dubu dari uku a wani filin shakatawa dake kusa da babban birnin Kasar.

Shugaba felipe Calderon da matarsa sun tarbi Paproma Benedict a filin saukar jiragen sama da kuma wasu matasa da suka iso daga bangarori da dama na Mexico.

Shugaba Calderon dai bai sumbaci zoben Paparomar ba kamar yadda wanda ya gada yayi a shekara ta dubu biyu da biyu.

Dandazon mutane ne dai sukai da fifi suna jiransa a kan tituna suna gandokin ganinsa, gashi an kwalla rana. Dubban mabiya ne da suka sanya fararen kaya da yaluwar riga da kuma kananan tutoci a hannunsu, sun jeru zuwa hanyar birnin Leon don ganin Paparoman.

An tsaurara matakan tsaro a kusa da Paparoman da yansanda da sojoji masu tarun yawa.

Paparoman dai na kai ziyarar ne a lokacinda ake artabu kan hana fataucin kwaya. Sai dai tuni ya yi magana a kan fadan Mexico kan kwaya inda yayi kira ga yan Mexicon da su yaki dabiar da ya kira abunda yake lalata matasa.

A tattaunawar da za suyi da shugaban kasar nan gaba za suyi magana sosai akan fadan. wasu batutuwa kuma da za su tattauna sun hada da yancin addini da kuma kariya ga iyali.

Karin bayani