Tarin huka yana kashe masu dauke da kanjamau

Maganin cutar tarin huka Hakkin mallakar hoto who
Image caption Tana halaka masu kanjamau

Yau ce ranar yaki da cutar tarin huka ta duniya, wadda ke da nufin kara fadakar da jama'ar duniya kan bukatar yaki da cutar domin kawar da ita.

Taken ranar ta bana dai shi ne 'Kawar da Tarin Fuka a Rayuwata', abin da ke jaddada muhimmancin ba da himma daga bangaren daidaikun mutane da kuma kungiyoyi da hukumomi wajen yakar cutar.

Hukumar Lafiya ta Duniya, WHO, ta ce kimanin kashi daya cikin uku na al'ummar duniya na dauke da kwayar cutar da ke haddasa ta.

Wani batu da ke tasowa a baya-bayan nan dai shi ne irin alakar da ke akwai tsakanin tarin na huka da kuma cutar kanjamau mai karya garkuwar jiki.

Babban dalili shi ne ganin yadda alkaluman hukumomi ke nuni da cewa yawancin masu fama da ciwon na kanjamau na dauke da tarin fuka kuma tarin na fuka na daya daga cikin abubuwan da akn yi sanadiyar mutuwar masu kanjamau.

Masana sun ce dalilin da ya san tarin na huka ke yawan kasha masu cutar kanjamau shi ne cewa ba su da kariya a jikinsu da za ta yaki tarin huka.

Karin bayani