An kama mai kera bindigogi a jihar Filato

Rahotanni daga jihar Filaton Nijeriya na cewa rundunar tsaro ta musamman mai aikin samar da zaman lafiya ta kama wasu rukunonin mutane wadanda take zargi da aikata laifukan keta haddin tsaro ciki harda wani mai kera bindigogi ba bisa ka'ida ba.

Rundunar dai ta shaida wa manema labarai a birnin Jos cewa ta kama mutanen ne a karshen makon nan kuma tana ci gaba da bincike.

Jihar ta Filato dai na daya daga cikin jihohin Nijeriya da suka fi fama da matsalar tsaro inda baya ga tashe-tashen hankula masu nasaba da kabilanci da addini da kuma siyasa, jihar ta kuma sha fama da hare-hare na bama-bamai.

Rundunar tsaron ta musamman mai aikin kyaye zamanl afiya a jihar ta Filato mai yawan fama da tashin hankali, ta bayyana cewa ta kama mutanen ne a wurare daban-daban a cikin jihar kuma suna zarginsu da aikkata laifuka daban-daban wadanda ked a hadari ga tsaron lafiyar al'uma.

Kakakin rundunar tsaro ta musammnan mai akin kiyaye zaman lafiya a jihar ta Filato, Captain Markus Mdayelyah, ya shaida mani cewa sun kama mutanen ne rukuni-rukuni, inda aka kama wani mutum mai suna Dung Bulus a kauyen Shen dake karamar hukumar Jos ta Kudu, wanda ake zargi da kera bindigogi bad a izini ba, kuma sun ma kama shi da wasu sabbin bindigogi guda uku day a kera.

Kakakin na rundunra tsaro, ya kuma shioda mani cewa dakarunsu su yi wanbi samamae a gidan Mista Dung Bulus a jiya inda yake kera bindigogin kuma suka ci nasarar gano sabbnin bindigogi da kuma wasu kayan aiki da yake amfani das u wajen kera bindigogi a kauyen na Shen.

Haka nan kuma runduna tsarin ta bayyana cafke wani mutum mai suna Alex Danladi, wanda ke gabatar da kansa a matsayin jami'in sojan Nijeriya a Gyel dake kusa da Bukur, kuma sun same ma shi Cikin kayan soja.

Ko baya ga wadannan mutane, kakakin na rundunar tsaro a jihar Filato Kfatin Markus, ya shiada mani cewa sun kama wasu dalibai biyu na jami'ar Jos dauke da karamar bindiga pistol, suna tuka wata mota Toyota Corolla

Binciken farko ya nuna masu cewa daliban masu suna Mista Babalke Bala da Mista Benjamin Umeh, sun kwace motar ce da bakin bindiga daga mai ita, yayin da su ma Tasiru Isa da Hasiya Muhammad, a cewar rundunar tsaron an kama su da motoci biyu na safa-safa suna kokarin tserawa da su a wajen jen gidan adana kayakin tarihi na Jos.

Hukumomin tsaron dai sun bayyana cewa suna ci gaba da bincike kan mutanen da suka kama da nufin gurfanar da su a gaban shari'a.

Wannan dai ba shi ne karon farko da aka kama mutane da makamai da kuma wuraren kera makmai a jihar Filato ba da wasu sassa na Nijeriya, amma kuma ba kasafai ake jin ana hukunta wadanda ake kamawa da aikata laifukan ba.

Ko a baya ma dai hukumomin tsaro sun kama wani rumbum makamai a karamar hukumar jos ta kudu, kana suka kama wani wurin kera bama-bamai a unguwar Millionaires Quarters a cikin birnin Jos amma kawo yanzu babu amo balle labarin inda aka kwana a binciken su bare a yi batun hukunci.