An kai hare-hare a Maiduguri

Image caption Ana binciken ababen hawa a Maiduguri

A Najeriya, mutane a kalla hudu ne rudunar tsaro ta JTF ta ce an kashe a wasu hare-hare da wasu 'yan bindiga suka kai yammacin jiya a birnin Maiduguri na jihar Borno.

An kai harin ne a kan caaji ofis na 'yan sanda dake Lamisla da wata cibiyar tsaro ta sojoji dake railway.

Kakakin rudunar tsaro ta JTF wato, Letftanal Kanal Sagir Musa ya ce sun kashe mahara hudu amma ya ki ya bayyana adadin jami'an tsaron da su ka rasa rayukansu ko kuma su ka jikkata.

Rundunar hadin gwiwa ta Jami'an tsaro a jihar ta ce wadanda suka kai ma sojojin hari ba su yi nasara ba.

Amma wasu majiyoyi sun ce sun ga a kalla gawawwaki shida wanda ake kyautata zato fararen hula ne.

Sakamakon harin dai jami'an tsaron sun hana daruruwan mutane isa gidajensu a daren jiya.

Birnin na Maiduguri dai na fama da hare-hare wanda ake dangantawa da kungiyar nan ta Boko Haram.