Obama ya kai ziyarar aiki Korea ta kudu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shugaba Obama ya kai ziyara birnin Soeul ne domin halartar taron a kan makamin nukiliya.

Shugaban Amurka Barack Obama ya kai ziyara iyakar nan da ake cece-kuce a kanta tsakanin kasashen koriya Koriya ta arewa da ta kudu.

Shugaba Obama ya kai ziyarar ce a lokacin wata ziyarar aiki da ya kai Korea ta kudu domin halartar wani taro a kan tsaron makamin nukiliya.

Mista Obama ya kai ziyara sansanin soji dake kan iyakar, mahadar da sojin Koriya ta kudu da ta arewa ke sintiri, kuma ana sa ran shugaba Obama zai gana da sojojin koriya ta kudu a wannan yankin.

Shugaba Obama zai kai ziyararce domin nuna goyon baya ga sojojin koriya ta kudu da kuma dakarun Amurka da su kai kusan sama da dubu ashirin da takwas a kasar.

Wanann dai na nuni da irin halin zaman zullimin da ake yi tsakanin kasashen koriya ta arewa da ta kudu.

Koriya ta arewa dai ba za ta halarci taron da ake yi a birinin Seoul ba.

Amma ana ganin taron zai maida hankali ne a kan dangantakar Washington da Pyongyang musamman ma kokarin da koriya ta arewa take yi na harba tauraron dan adam a sararin samaniya a watan da zamu shiga.

Jami'an Amurka dai sun bayyana cewa Shugaba Obama zai tayar da batun a wata tattaunawa da zai yi da shugabanin China da kuma Rasha.