An yi zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a yau a Senegal

Zabe a Senegal Hakkin mallakar hoto x
Image caption Ba a san maci tuwo ba...

Jama'ar kasar Senegal sun kada kuri'ar zaben shugaban kasar zagaye na biyu.

Shugaba mai ci, Abdullahi Wade, yana neman wa'adi na uku ne, abin da ake ta takaddama a kai.

‘Yan adawa suna cewa hakan ya saba wa tsara mulkin kasar, wanda ya babu shugaban da zai wuce wa’adi biyu a mulki.

Sai dai Kotun Kolin kasar ta ba Shugaba Wade damar tsayawa karo na ukun bisa cewa hanin bai shafi shi ba.

Yana dai fafatawa ne da tsohon Firaministansa, Macky Sall.

Ba a sami wani tashin hankali ba a lokacin yakin neman zaben zagaye na biyun, bayan da aka kashe akalla mutane shidda a zanga-zangar da akai ta yi gabanin zagayen farko na zaben, wanda aka yi ranar ashirin da shida ga watan Fabrairu na bana.

Masu kada kuri'ar dai sun ce zaben na gudana lami lafiya.

Karin bayani