Shugaba Wade ya sha kaye a zaben Senegal

Mutumin da ya lashe zaben Shugaban kasa a Senegal Macky Sall ya ce nasarar da ya samu wani sabon babi ga mutanen kasar ta Senegal.

Image caption Hotunan takarar Macky Sall da Abdullaye Wade

Mr Sall din yana magana ne jim kadan bayan shugaban kasar mai ci yanzu Abdullahi Wade ya amsa kayen da ya sha a zaben, bayan kokarin da ya yi na zama shugaban kasa a karo na uku a kasar.

Shugaba Wade dai ya yiwa kudin tsarin mulkin kasar gyaran fuska ne saboda ya samu damar kara tsaya takara a karo na uku a kasar.

Dubban magoya bayan Mista Mr Sall din dai sun fantsama a kan titunan birnin Dakar suna murna nasarar da ya samu a kan Abdullahi Wade a zaben zagaye na biyu.

Jim kadan bayan kammalla zaben ne Mista Wade ya amince cewa ya sha kaye a zaben da aka gudanar a jiya, amma a hukumar zaben kasar dai ba ta bayyana sakamakon zaben ba ya zuwa yanzu.

Mista Sall wanda ya yi nasara a kan Shugaban Wade ya ce nasararsa wani sabon babi ne ga al'ummar kasar, saboda ya ce a karon farko al'umar kasar za su ci gajiyar demokradiyyar.

Tun da kasar Senegal ta samu 'yan ci kai a shekarar 1960 ta ke gudanar da zaben, kuma ita ce kawai yammacin Afrika da ba'a taba gudanar da juyin mulki ba.

Shugaban Wade ya taka rawar ganin a wasu nasarorin da kasar ta samu ta bayan da ya lashe zabe a shekarar 2000.

Amma masu sukar gwamnatinsa sun ce dai Shugaba Wade ya gaggawara cika alkawuran da ya dauka na habbaka rayuwar al'mmar kasar.