Annan ya ce ya samu hadin kai daga Syria

Kofi Annan a China Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Wakilin Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan a China

Wani mai magana da yawun Kofi Annan, wato wakili na musanman da Majalisar Dinkin Duniya da Kungiyar Kasahen Labarawa suka tura Syria, ya ce kasar ta Syria ta amince da sharuddan da aka shimfida guda shida don kawo zaman lafiya a kasar.

Shirin zaman na lafiya dai ya kunshi janye sojojin gwamnati a garuruwan 'yan adawa, da kuma baiwa kungiyoyin agaji damar shiga kasar—duk a karkashin kulawar Majalisar ta Dinkin Duniya.

Sai dai mai magana da yawun na Kofi Annan ya ce nasarar shirin ta danganta ne a kan yadda aka aiwatar da shi.

Wani waklin BBC ya ce 'yan adawa sun yi maraba da shirin, sai dai a bayan fage wadansu da dama na nuna shakku a kansa, ganin yadda a baya wadansu shirye-shiryen suka kasa kawo zaman lafiya a kasar.