'Ya kamata Cuba ta sake gina sabuwar al'umma'- Paparoma

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Paparoma Benedict

Paparoma Benedict ya yi kira ga 'yan kasar Cuba su sake gina wata sabuwar al'umma kuma mai saukin sha'ani.

Paparoma Benedict ya bayyana hakan ne a lokacinda yake addua a gaban dubun-dubutan mutane a birnin Santiago na gabashin kasar ta Cuba

Wannan ne dai ziyara ta farko da ya kai kasar mai bin tafarkin gurguzu.

Cikin mutanen da suka hallara a wurin addu'ar har da jagoran 'yan kasar ta Cuba Raul Castro wanda ya saurari Paparoman yana jaddada muhimmancin addini da 'yanci.

Shugaba Castro din ya fada tun farko cewar Cuba ta bayar da cikakken 'yanci na addini kuma tana da kyakkyawar hulda da Cocin Catholika.