'Kano ce kan gaba wajen safarar miyagun kwayoyi'

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Haramtattun kwayoyi

A Najeriya, Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi wato NDLEA ta ce daga shekara ta 2011 zuwa bana ta samu nasarar kwace hodar Ibilis da kudinta ya kai naira biliyon 31.

Hukumar ta kuma bayyana cewa jihar Kano ce a Najeriya ta ke sahun gaba a kasar wajen safarar miyagun kwayoyi inda kuma jihar Lagas ke biye da ita.

Shugaban Hukumar, Alhaji Ahmadu Giade ya shaidawa BBC cewa yawan aikata laifukka da ake yi a jihar Kano na da nasaba da shan haramtattun kwayoyi.

Alhaji Giade ya ce jihar Ondo ce take kan gaba, cikin jihohin da ake kama wadannan miyagun kwayoyi saboda a nan ne ake nomanta sai kuma jihar Edo wadda ke biye.

Shugaban Hukumar yaki da manyan laiffuffuka na Burtaniya Mr. David Armand lokacin da ya jagoranci wata tawagar kwararru ta fuskar tsaro da suka ziyarci hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Nijeriyar, ya ce Nijeriya da Brittaniya za su ci gaba da aiki tare wajen ganin an magance yaduwar fataucin miyagun kwayoyi.