Ana ci gaba da ce-ce kuce akan sace kudin pansho

jonathan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

A Najeriya, ana ci gaba da ce-ce-ku-ce a kan zargin badakala da almundahana da dubban miliyoyi naira na kudaden fanshon ma'aikatan kasar.

Rahotanni dai na nuna cewa hatta 'yan kwamiti na musamman wanda aka kafa don yin gyara a harkar ta fansho sun fada cikin zargin na almundahana.

Ma'aikatan da suka yi ritaya a kasar ta Najeriya kan koka da irin matsanancin halin da su kan shiga sakamakon rashin biyansu kudaden fansho wadansu ma kan rasa rayukansu yayin neman hakkin nasu.

A wani taron manema labarai da kwamitin na musamman ya kira, mai magana da yawunsa, Hassan Salihu, ya musanta zargin almundahana da kudaden fanshon 'yan sanda har naira miliyan dubu ashirin da hudu da aka danganta da rahoton wani kamfanin binciken kudi mai zaman kansa na kasa-da-kasa mai suna KPMG, zargin da aka danaganta da shugaban kwamitin, Abdul-Rasheed Maina.

Sai dai a yayinda BBC ta nemi jin ta bakin wani daga cikin jami'an kamfanin binciken na KPMG don tantance sahihancin rahoton, bai tabbatar da rahoton, wanda wata jarida ta Najeriyar ambato, ya yi zargin ba.

A cewarsa duk wani rahoto da suka fitar suna danka shi ne ga hukumomin gwamnatin da al'amarin ya shafa kawai.

Karin bayani