Ana tuhumar Strauss Khan a Faransa

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Dominique Strauss Khan

Kasar Faransa ta fara bincikar tsohon Shugaban asusun ba da lamuni na duniya IMF Dominique Strauss Khan bisa zargin da ake na hannun sa a wata Kungiya dake nemo karuwai ga masu bukatar shagulgula.

An shirya jerin laifukka na share fage da za a tuhume shi da su bayan alkalan Kotun Majistare sun yi masa tambayoyi a birnin Lille.

Tuhume-tuhumen da ake yiwa ya ta'allaka ne a kan hulda da ya yi da wata kungiya mai daukar mata masu zaman kansu aiki inda ake shagulgular nishadantarwa da su a wasu manyan Otel a birnin Lille da Paris da kuma Washington a lokacin da yake shugabanciN asusun bada lamuni na duniya.

Kusan mutane takwas ne yanzu haka ake bincike akan su game da wannan aika aikar, daga ciki har da wani babban jami'in 'yan sanda.

Mista Strauss Khan dai bai musanta cewa ya halarci shagulgulan ba, ya dai musanta cewa ya san matan da su ke wurin karuwai ne.

Lauyan Mistan Khan dai ya ce babu yadda Strauss Khan zai gane cewa karuwaine a wurin shagulgulan saboda irin shigar da su ka yi.

Alkalan da ke tuhumar Strauss Khan suna na da shaidun sakonnin wayar salula da wasu daga cikin matan da su ka halarci wadannan shagulgula su ka mika musu inda suke ikirarin cewa Strauss Khan na da masaniyar cewa suna zaman kansu ne.

A gobe Laraba ma, Mista Khan zai bayyana a gaban wata kotu a birnin New York domin amsa tuhuma game da zargin yunkurin yin fyade ga wata ma'aikaciyar Otel a Amurka.