Amurka na taka tsan tsan akan Syria

annan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kofi Annan da Shugaba Bashar Al Assad

Amurka ta yi taka tsan tsan a irin martanin da ta mayar ga amincewar da Syria ta yi da shirin zaman lafiya da manzon Majalisar dinkin duniya Kofi Anan, ya gabatarwa Syriyar.

Ma'aikatar harkokin wajen Amurkar ta ce wannan mataki ne mai muhimmanci idan anyi fada da cikawa.

Kofi Annan yace dole ne Syria ta kawo karshen zubda jinin da akeyi ta kuma bari masu aikin agaji su shiga kasar.

Majalisar dinkin duniya ta ce yawan mutanen da suka mutu a rikicin Syria a shekara daya data wuce yanzu ya kai dubu tara.

Wani manzon Majalisar dinkin duniya zuwa gabas ta tsakiya, Robert Serry ya shaidawa kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniyar cewa tashin hankali ya ci gaba a Syria ba kakkautawa.

Robert Seery yace "Ana bukatar daukan matakan gaggauwa daga gwamnatin Syria, akan alkwaurran da ta dauka da kuma nunawa jama'ar Syria cewa, a shirye take wajen kawo karshen hankalin da ake fama da shi".

A baya dai, Majalisar Dinkin Duniyar ta ce mutane kamar dubu takwas ne suka mutu a fadan na Syria.

Karin bayani