ECOWAS ta yiwa shugabannin sojin Mali barazana

mali Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Shugaban mulkin sojin Mali, Amadou Haya Sanago

Shugabannin mulkin sojin Mali sun ce zasu fara aiki da wani sabon kundin tsarin mulkin kasa, jim kadan bayan kungiyar raya tattalin azrikin kasashen yammacin Afrika ta takakarda ita saboda juyin mulkin da suka yi a makon jiya.

A Wani jawabi ta gidan telbijin, sojojin sun yi alkawarin mutunta, 'yancin fadin albarkacin bakin jama'a da kuma walwala.

Sai dai babu batun lokacinda za a mika mulki ga gwamnatin da aka hambararr.

Shugaban Ivory Coast, Alassan 0uatara yace ya shaidawa wata tawagar sojojin da taje kasar sa cewa dole ne a dawo da tsarin dimokiradiyya.

A taron gaggawa da aka yi, kungiyar ECOWAS tayi shellar cewar zata aike da wata tawaga zuwa kasar Mali , wadda dakarun wanzar da zaman lafiya na kungiyar zasu mara ma baya.

Shugaban hukumar ECOWAS, Kadre Desire Querdarogo yace "taron ya bada izini ga dakarun kungiyar akan su kasance cikin shirin ko ta kwana . Idan shugabanin soja na kasar Mali sun ki yin biyaya akan shawarar da aka yanke".

Matsayar da kasashen yammacin Afrika suka cimma ta kasance manuniya akan abubuwan da suka faru a watan Junairun bara.

A wancan lokacin dai Laurent Gbagba ya ki sauka daga kan karagar mulki bayan ya sha kaye a zaben shugaban kasar Ivory Coast da aka yi.

Haka zalika a wancan lokacin shugabannin yankin sunyi balaguro zuwa Ivory Coast kuma sunyi barazanar amfani da karfin soja.

Karin bayani